Kotu ta ce a biya sarkin Kano Murabus diyya | BATUTUWA | DW | 30.11.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kotu ta ce a biya sarkin Kano Murabus diyya

Martani da tofa albarkacin baki dangane da hukuncin wata babbar kotun tarayya a Abuja Najeriya, na yin watsi da matakin tilastawa sarkin Kano mai murabus Muhammadu Sanusi na II yin gudun hijira.

Nigeria - Emir von Kano - Muhammadu Sanusi II

Sarkin kano mai murabus Muhammadu Sanusi II

Babbar kotun ta tarayya da ke Abuja fadar gwamnatin Najeriya, karkashin jagorancin mai shari'a Anwuli Chikere ta zartas da hukuncin cewa tilastawa Muhammadu Sanusi na II yin hijira a kauyen Loko kafin daga bisani a mayar da shi Awe a jihar Nasarawa da ke yankin tsakiyar Najeriyar, haramtaccen aiki ne wanda ya yi katsalandan ga yancinsa na walwala.

Karin Bayani: Kungiyar Amnesty ta ce a mutunta 'yancin Sanusi

Kotun ta ce lallai gwamnatin Kano ta fito karara ta bai wa sarkin hakuri ta kuma wallafa wannan neman afuwa a jaridun kasar guda biyu, kana ta kirga Naira miliyan 10 ta damka su ga sarkin sakamakon batancin da aka yi masa, tun wancan lokaci. Muhammadu Sanusi ya karbi kaddarar tube shi da aka yi daga sarautar amma a kan batun tilasta masa yin gudun hijira sai ya tunkari kotun domin neman hakkinsa, lamarin da ya kawo wannan hukuncin da kotun da aka zartas.

Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje

To ko me wannan hukunci yake nufi kuma me ye matsayin masana shari'a a kai? Barrister Abba Hikima Fagge lauya mai zaman kansa a Kano, ya bayyana cewa da ma al'adar hana tubabben sarki watayawa haramtacciyar doka ce wacce sam ba ta dace ba dan haka hukuncin ya dace da kundin tsarin mulkin kasa. To amma gwamnatin Kano ta bakin alkalin alkalai kan kwamishinan shari'a na jihar Barrister MA Lawal ta ce, za ta nazarci hukuncin tare da daukar matakin daukaka kara kuma a shirye take ta tsaya gam domin tabbatar da kare martabar masarautun jihar ta Kano.

Karin Bayani: Masarautar Kano a idon duniya

Tuni dai magoya bayan Sarki Muhammad Sanusi na II mai murabus, suka shiga murna da nuna goyon baya har ma wani makusancin sarkin Alhaji Bashir Ungogo ke cewar a jira su nan da dan lokaci kadan sarkin zai shigo Kano. Wannan hukunci dai ya zowa gwamnatin Kanon a yanayi marar dadi, domin shi ne karo na biyu da ake zartar da hukunci kan ta biya diyya ko kuma ranko. Idan ba a manta ba kwannann gwamnatin ta biya naira dubu 800 ga dan jaridar nan Jafar Jafar sakamakon bata masa lokaci da wata kotu ta ce an yi, a kan kara da aka kai shi, bayan rahotan faifen bidiyon nan da ya saki wanda gwamnati ta kalubalanta.

Sauti da bidiyo akan labarin