1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhammadu Sanusi II ya dawo sarautar Kano

Abdoulaye Mamane Amadou
May 23, 2024

Sarki Muhammadu Sanusi ÍI ya sake dawowa matsayinsa, bayan rusa marautun jihar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf mai ci ta yi a wannan Alhamis.

https://p.dw.com/p/4gDKt
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi IIHoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

Bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta sake yi wa dokar masarautun jihar gyaran fuska a cikin gaggawa, daga karshe mahukuntan jihar Kano sun sake dawo da Muhammad Sanusi na biyu a matsayin sarkin Kano.

Wannan na zuwa ne bayan dogon lokacin da aka kwashe ana jita-jitar hakan za ta faru, kana tuni 'yan majalisa na jam'iyyar adawa ta APC suka yi watsi da sabuwar dokar da suka ce za ta kuntata wa mutanen karkara wadanda tun da farko tsohuwar gwamnatinsu ta ce ta rarraba masarautar domin su.

Karin bayani :  Kirkirar masarautu a Kano ta haifar da mahawara

Yadda ta kaya a majalisar dokokin Kano

Kunshin dokar bashi da wani dogon turanci domin karara ya bayyana cewar a koma gidan jiya (ma’ana dai ungulu ta koma gidan ta na tsamiya) inda aka ajiye dokar nadin sabbin sarakuna wacce aka yi ta ranar biyar ga watan Disambar 2019, da kuma wacce aka yi a ranar takwas ga watan Mayun shekarar 2019, wato dokokin da suka nada sabbin sarakuna hudu da kuma sauke sarkin Kano Muhammad Sunusi II.

Gwamnan Jihar Kano  Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir YusufHoto: Sanusi Bature

Karin bayani :  Sanusi Lamido Sanusi sabon sarkin Kano

Masu mukamai a masarautar Kano na cikin damuwa

Alhaji Aminu Babba Dangundi shi ne sarkin Dawaki Babba a masarautar Kano, guda daga cikin manyan masu rike da sarautun da wananan doka ta yi awon gaba da kujerun su, ya ce abin bai yi dadi ba kuma ba za su amince ba.

 Ana tsaka da muhawara a kan dokar sai yan majalisar jamiyyar adawa ta APC suka fice daga majalisar tare da fatali da matakin dokar.