Sarauniyar Ingila ta jaddada bukatar hadin kai a Turai | Labarai | DW | 25.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarauniyar Ingila ta jaddada bukatar hadin kai a Turai

Sarauniya Elizabeth ta yi wannan furucin ne a birnin Berlin, a ci gaba da rangadin aikin da take yi a Tarayyar Jamus na kwanaki hudu.

Basarakiyar ta Ingila ta jaddada bukatar hadin kai tsakanin kasashen Turai. A cikin shekaru biyu masu gabatowa ne dai, Britaniya zata kada kuri'ar raba gardama dangane da matsayinta na ci gaba da kasancewa a cikin Kungiyar Tarayyar Turai.

Sarauniyar ta yi wannan jawabi ne a bainar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da fraiministan Britaniya David Cameron, inda ta ce rarrabuwar kawuna tsakanin turai yana da babbar illa ga gamayyar kasashen.

Shugaban kasar Jamus Joachim Gauck ya ce tattaunawa mai ma'ana dangane da gyare-gyaren da Britaniya ke muradin gani a nahiyar Turai yana da muhimmanci, inda ya kara da cewar Kungiyar Tarayyar Turai na bukatar wakilcin Ingila.