Sanusi Lamido Sanusi sabon sarkin Kano | Siyasa | DW | 10.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sanusi Lamido Sanusi sabon sarkin Kano

Gwamnatin jihar Kano tatattabar da zaben Sanusi Lamido Sanusi tsohon gwamnan babban bankin Najeriya a matsayin sabon sarkin Kano na 14.

A dazu-dazun nan ne fadar gwamnatin jihar Kano ta fiddo sanarwar nadin tsofon gwamnan babban bankin Tarayyar Najeriya Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sabon sarkin Kano na 14, wanda zai maye gurbin marigayi Alhaji Ado Abdullahi Bayero da ya rigamu gidan gaskiya a ranar Juma'a da ta gabata, yana dan shekaru 83 da haifuwa, bayan da ya shafe shekaru 51 kan karagar mulkin masarautar ta Kano.

Sabon sarkin Kano

'

Lamido Sanusi

Sai dai kuma kafin wannan sanarwa ta gwamnatin Kano, masu kula da zaben sabon sarkin dake fada sun nuna amincewar su ce ga Sanusi Lamido Ado Bayero wanda yake da ne ga marigayi Alhaji Ado Bayero, wanda hakan a halin yanzu, ya janyo cecekuce mai yawa a birnin na Kano har ma da kona tayoyi daga bengaran masu goyon bayan nadin Dan marigayin, wadanda suka ce ba su yarda ba da wannan nadi da fadar gwamnatin ta Kano ta fito da shi ba.

Sai dai kuma dama a dokance, gwamnatin ta Kano ce ke da nauyin bayar da amincewar ta ga sabon sarkin da aka zaba.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin