Ado Bayero marigayi sarkin Kano a arewacin Najeriya wanda ya yi mulki daga 1963 zuwa lokacin da ya rasu a shekara ta 2014.
Yana cikin masu rike da sarautun gargajiya da ake mutuntawa a lokacin rayuwarsa, kuma ya bar 'ya'ya masu yawa. Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi ya gaji sarautar daga Marigayi Ado Bayero.