Sankarau ta kashe muta ne 400 a Nijar | Labarai | DW | 16.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sankarau ta kashe muta ne 400 a Nijar

Kungiyar kula da lafiya ta duniya wato WHO ta bayyana cewa cutar sankarau na bazuwa a cikin sauri da rubi biyu, lamarin da ke zama wani abun tada hankali .

Kungiyar WHO mai helkwata a birnin Geneva ta bayyana cewa, yanzu haka sama da mutane 400 suka mutu sakamakon cutar ta Sankarau a kasar ta Nijar. Inda kugiyar ta ce kama daga watan Junairu, kawo ranar Jumma'a da ta gabata 15.05.2015. Muta ne 6,179 suka kamu da cutar, inda wasu 423 suka mutu. A Yamai babban birnin kasar, mutane 4,99 suka kamu da Sankarau, kuma a Yamai din kaiwa, kungiyar ta ce mutane 226 cutar ta hallaka. Kawo yanzu dai kungiyoyin agaji kamar na likitoci mai suna Médecins Sans Frontières ko kuma Doctors Without boarders, sun aika da jami'ansu don kawo ma hukumonin Jamhuriyar Nijar dauki.