Samun galaba a yaki da Ebola | Labarai | DW | 29.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Samun galaba a yaki da Ebola

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cewa kwararru a fannin lafiya sun mayar da hankali wajen kawo karshen yaduwar annobar cutar Ebola mai saurin kisa maimakon rage yaduwarta.

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa a karon farko tun cikin watan Yuni, a makon da ya gabata an samu raguwar wadanda ke kamuwa da cutar a kasashe uku da cutar tafi kamari a cikinsu wato Guinea da Saliyo da kuma Laberiya. Hukumar ta kara da cewa kaso 30 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar a Guinea da kuma kaso 50 cikin 100 a Laberiya ne kadai aka hakikance sun yi mu'amala da masu cutar ta Ebola, wanda hakan ya sanya tunanin a kan yadda mutane ke kamuwa da ita. Cutar dai kawo yanzu ta hallaka sama da mutane 8,000 tun bayan da ta bulla a yankin yammacin Afirka cikin farkon shekara ta 2014 da ta gabata.

MAwallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu