Samo mafita a taron sauyin yanayi | Labarai | DW | 11.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Samo mafita a taron sauyin yanayi

A wannan Asabar 12 ga watan nan na Disamba da muke ciki ne za a kammala taron sauyi ko kuma dumamar yanayi da yake gudana a yanzu haka a birnin Paris na kasar Faransa.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

Tun da farko dai an shirya cewa za a kammala taron ne a ranar Jumma'a 11 ga watan na Disamba, sai dai rashin cimma matsaya kan wasu batutuwa da suka hadar da rage zafin da duniya ke fama da shi, ya sanya mahalartar taron kara wa'adin kammala taron da kwana guda. Da yake bayyana nasa ra'ayin kan taron sauyi ko dumamar yanyin na kasar Faransa, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon cewa ya yi:

"Ina neman duk masu tattaunawa kan wannan batu su bayyana ra'ayinsu. Wannan ba lokaci bane na tsayawa kan ra'ayin kasarka, samun mafita da za ta amfani duniya duniya baki daya za ta taimaka wajen samar da mafita a ko ina."

Sabon kundin da ake son amincewa da shi a yayin taron na birnin Paris dai ya kunshi batutuwa da suka hadar da batun kayyade adadin zafin da duniya ke fuskanta zuwa digiri biyu a ma'aunin celsius, ko da yake kananan Tsibirai da ke fuskantar babbar barazana daga dumamar yanayin na bukatar a rage zafin zuwa digiri daya da rabi a ma'aunin nan Celsius.