Samar da makewayi mai tsabta a karkarar jihar Tahoua | Himma dai Matasa | DW | 13.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Samar da makewayi mai tsabta a karkarar jihar Tahoua

A Jamhuriyar Nijar kungiya mai zaman kan ta ta IDELA mai cibiya a birnin Tahoua ta dukufa wajan fadakar da mutanan karkara samun makewayi na zamani domin yaki da cututuka.

Abdul Naser Abubakar, matashi ne dan kimanin shekaru 38 da haifuwa, ya kuma dukufa ne ga canzawa mazauna karkara tunani ta hanyar wayar da kawunansu domin kyautata rayuwarsu, kuma ya share sama da shekaru 15 a nahiyar Turai inda ya soma aiki bayan kammala karatunsa, to amman kuma sai ya dawo gida Nijar domin ya bada irin tashi gudunmuwa ga neman kyautata rayuwar al'umma a yankin jihar Tahoua da ke Arewacin kasar ta Nijar.

Kungiyar ta IDELA (Initiative pour le Developpement Local en Afrique) da Abdul Naser Abubakar ke jagoranci, Ma'ana Fusahata don bunkasa yankunan karkara a Afirka, ta kunshi ma'aikata 20 da ke da cibiyarta a birnin Tahoua, wadanda daga cikinsu mutun 10 ke tafiya cikin karkara domin fadakarwa, kowane kuma na da babur dinsa kamar musali a garin Ajaga cikin karamar hukumar Tebaram da ke da tazarar kilometa 110 daga birnin Tahoua inda Abdul Naser Abubakar ke wayar da kan mazauna garin.

Sauti da bidiyo akan labarin