1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Saliyo za ta daina hukuncin kisa

July 24, 2021

Majalisar dokokin kasar Saliyo, ta amince da dokar haramta hukuncin kisa inda Saliyon ta zama kasa ta farko a Afirka da ta fara yin fatali da hukuncin mai tsanani.

https://p.dw.com/p/3xzG8
Sierra Leone, Freetown: Der Präsident Julius Maada Bio erklärt Notstand wegen Vergewaltigung und sexueller Gewalt
Hoto: Reuters/C. Inveen

Akasarin 'yan majalisar da suka yi zama a kan batun a ranar Juma'a ne suka zabi yi wa hukuncin na kisa kwaskwarima a kasar ta Saliyo, abin da ya sanya za ta zama abin misali a nahiyar Afirka.

Maimakon yanke wa mai laifi hukuncin na kisa, yanzu an maye shi da daurin rai-da-rai ko kuma karanci zaman shekaru 30 a gidan yari.

Tun a shekara ta 1998 ba a sami wani da aka yanke wa hukuncin kisa ba a kasar ta Saliyo, duk da cewa ana aikata laifuka da suka kamaci hakan.

Tsarin mulkin kasar na shekarar 1991 ya amince da hukuncin kisa a kan 'yan fashi da wadanda suka aiakata kisa da cin amanar kasa da ma sojojin da suka yi wa shugabannisu bore.