Sakataren harkokin wajen Amirka zai fara rangadin farko a Turai | Labarai | DW | 25.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakataren harkokin wajen Amirka zai fara rangadin farko a Turai

A wannan Litinin John Kerry ke isa biranen London da Berlin a rangadinsa na farko zuwa ketare, tun bayan da ya dare kan wannan mukami a wannan wata.

Wannan rangadin na sabon sakataren harkokin wajen na Amirka John Kerry dai zai kai shi kasashe da yawa a nahiyar Turai kafin ya ci gaba zuwa yankin Gabas ta Tsakiya da kuma nahiyar Afirka. Tsohuwar sakatariyar harkokin waje Hillary Rodham Clinton wadda Kerry ya gada, ta kai ziyarce ziyarce kasashe da yawa a matsayin sakatariyar harkokin wajen Amirka lokacin wa'adin farko na mulkin shugaba Barack Obama. Obama ya lashe zaben yin tazarce a wa'adi na biyu a watan Nuwamban shekarar 2012, kuma an rantsar da shi a cikin watan janeru. A ranar Litinin da dare ake sa ran isowarsa birnin Berlin inda zai gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da takwaransa na Jamus Guido Westerwelle. A ranar Talata a karon farko zai gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrova birnin Berlin. Wannan ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin gwamnatocin Washington da Mosko ke kara yin tsami saboda rikicin Syria.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe