Sakamakon Binciken Yakin 2006 a Lebanon | Siyasa | DW | 30.01.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon Binciken Yakin 2006 a Lebanon

Rahotan sakamakon binciken yakin Izraela da Hizubollahi na Lebanon

default

Shugaban komitin bincike, Eliyahu Winograd


A yau ne komitin binciken da gwamnatin Izraela ta naɗa domin binciken yaƙin daya gudana tsakanin Dakarun ƙasar da 'yan Hizobullahin Lebanon a shekara ta 2006 ya gabatar da rahotan dake nunar da gazawa a ɓangarorin magabatan siyasa da tsaron ƙasar,sai dai Primiya Ehud Olmert bai nuna almun yin murabus daga mukamin sa ba.

Daya ke gabatar da Rahotan da yammacin yau,Shugaban Komitin binciken kuma tsohon Alkalin Izraelan Eliahu Winograd,yace an gano kura kurai da dama a bangaren mahunkutan Izrelan a siyasan ce da fannin tsaro.

Ya bayyana yaƙin daya ɗauki tsawon wata guda yana gudana tsakanin Dakarun Izraelan da 'yan Hizobullahin Libanon ɗin, a matsayin wani tabargaza ne da haifarwa da Izraelan wani ɗa mai iadanu ba face asara.

To sai dai Primiya Ehud Olmert wanda ya tsallake rahotan wucin gadi da komitin ya gabatar a watan Aprilu,ya bayyana a fili cewar bashi da niyyan ajiye mukamin nasa,kuma tun da safiyar yau ɗin ne ya samu goyon baya daga takwarorinsa dake gwamnatin haɗin kana kasa a Izraela.

"Yace duk da waɗannan kura kurai da wannan komiti ya gano dangane da yakin da muka gwabza da Libanon,bani da nufin sauka daga matsayi na na Primiyan wannan kasa ,tunda mun yi munyi gyaran kura-kuran da mukayi "

Jim kaɗan da Olmert ya karɓi rahotan komitin ,kafin a gabatarwa dashi wa jama'a,majiyar siyasa na nuni dacewar na hannun primiyan sunyi farin ciki da sakamakon wannan bincike,musamman karshen rahotan dake nuni da yadda Olmert ya zartar da hukuncin kaddamar da yaƙin,wanda kuma hakan ne ya kasance batun dake sarkakkiyyar gaske dangane da wannan yaƙi.

Abokan adawa ta karkashin kasa dai sun sha kokarin neman magoya baya dangane da kama madafan iko,adangane da zargin yiwuwar yin murabus din Ehud Olmert daga matsayin shugaban gwamnatin na Izraela,dangane da sakamakon wannan bincike.

To sai dai duk dacewar bashi ta farin jini ta fannin kuria'ar ra'ayin jama'a,wanda tuni yayi asarar daya daga cikin wadanda suke gwamnatin hadin kan kasa dashi a wannan watan ,sakamakon yunkurin sa na sasantawa da Palastinu ,Primiyan Izraelan bashi da tsayayyen Dan takara dazai iya kalubalantar sa.

Bugu da kari yana da cikakken goyon bayan shugaba George W Bush na Amurka ,wanda ɓarkewan rikicin siyasa a Izrelan zai tarwatsa fatan sa na warware rikicin yankin kafin cikan wa'adinsa kan karagar shugabancin Amurkan .

Olmert yace tuni ya aiwatar da shawarwarin da komitin ta bayar tun a rahotan ta na farko kuma yanzu akwai zaman lafiya a yankin arewacin wannan kasa..

"A yau koina ya kasance cikin lumana a yankin arewacin wannan ƙasa.Bawai na rana ɗaya,ko wata guda ba,amma hakan ya kasance cikin tsawon watanni 18 da suka gabata .Hakan na mai zama lokaci mafi tsawo da aka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin arewacin kasar cikin shekaru 25 da suka gaba"

Tuni dai Hafsan sojin Izrelan da Ministan tsaro suka ajiye mukaman su a bara ,a wani abunda manazarta ke gani a matsayin ihu bayan hari ,tunda 'yan Hizobullahin sun cafke dakarun Izraelan biyu ,tare da kashe wasu 8 a wani harin kan iyakoki da suka kai.

Rahotan na yau,sabanin na wucin gadin da aka gabatar a watan Afrilu ,ya mayar da hankali ne kan kwanakin karshe na yakin daya dauki tsawon wata guda yana gudana,lokacin da Olmert ya bada umurnin aikewa da dakarun kasa ,duk da yarjejeniyar da Majalisar Dunikin duniya ta cimma na kawo karshen yakin daya kashe akalla Fararen hula 900 na Libanon,da mayaka 300.

Ayayin da Izrelan tayi asaran mutane 159 mafi yawan su sojoji,batu da 'yan siyasa daga jamiiyyun adawa da 'yan uwan mamatan suka ce zai haifar da zanga zanga cikin wannan makona Izraelan.


 • Kwanan wata 30.01.2008
 • Mawallafi Mohammed, Zainab
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CzzB
 • Kwanan wata 30.01.2008
 • Mawallafi Mohammed, Zainab
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CzzB