Sabuwar makarantar horas da Limamai a Berlin | Zamantakewa | DW | 02.04.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Sabuwar makarantar horas da Limamai a Berlin

A ƙarshen watan Maris da ya gabata aka buɗe wata babbar makarantar horas da Limaman addinin muslunci cikin harshen Jamusanci a unguwar Lichtenberg dake a birnin Berlin.

default

Horas da Limaman Islama a Berlin

Ɗaliban dake zaman limaman goben, a nan Jamus suka girma kuma za su kasance wata gada tsakanin gamaiyar musulmi a Jamus da kuma al´umar ƙasar. Waɗannan matasan ´yan shekarun haihuwa tsakanin 18 zuwa 25 sun fito ne daga sassa daban daban na tarayyar ta Jamus. Gabanin fara wannan kwas sai da aka yi wani kwas na sharen fage kuma aka buga a shafin yanar gizo na wannan makarantar mai zaman kanta da ake kira Buhara. Shirin Taɓa ka Lashe a wannan makon ya kai ziyara a makarantar dake a unguwar Lichtenberg dake Berlin.

Kawo yanzu kimanin kashi 90 cikin 100 na Limamai a nan Jamus ana kawo su ƙasar ne ta hannun uwar ƙungiyar Turkawa a Jamus wato DITIB. Da yawa daga cikinsu na samun horo ne a ƙasar Turkiya kuma ba su da wata cikakkiyar masaniya game da rayuwa a nan Jamus kana kuma ba su iya harshen Jamusanci ba. A saboda haka sabuwar makarantar horas da Limaman da aka buɗe a birnin Berlin za ta ba da gudunmawa don ganin an samu canji bisa manufa. Shugaban makarantar Alexander Weiger ya ce horon wanda mafi yawa za a yi shi a cikin harshen Jamusanci, za a ɗauki shekaru shida kafi ɗalibi ya sauke karatu.

“A shekaru uku na farko za a fara koyar da harshen Larabci, karatun al-Qur´ani da kuma na addini. Ta haka za a taimakawa ɗaliban domin su samu sauƙin fahimtar darussa a shekaru ukun ƙarshe na neman ilimi mai zurfi. Muhimmin abu a wannan makaranta ta mu shi ne darussan Jamusanci da na tsarin zamantakewa ta wannan al´uma, domin a shirya ɗalibai yadda za su samu ƙarfin guiwar tinkarar ƙalubalen wannan ƙarni na 21 musamman a Jamus mai ƙunshe da al´umomi daban daban.”

Shugaban makarantar Alexnader Weiger wanda ya musulunta, shi kanshi karatun fannin kimiyar siyasa yayi a jami´a, yanzu haka dai ne yana koyar da harshen Jamusanci da ilimin mu´amala da zaman jama´a a makarantu. Yayi nuni da cewa yanzu haka ɗalibai 29 sun fara neman ilimin ta shafin yanar gizon makarantar kuma nan gaba kaɗan za a samu wuri a ajujuwa biyu na makarantar. To sai dai horon da za a bawa matasan a wannan makaranta mai zaman kanta ba kyauta ba ne. A duk shekara kowane ɗalibi zai biya euro 4000 a matsayin kuɗin makaranta.

Tun a shekara ta 2004 aka fara aikin gina makarantar a harabar wani gidan al´adu da aka yiwa kwaskwarima. Shugaban makarantar Alexander Weiger ya nuna gamsuwarsa da samun nasarar kammala wannan aiki yana mai cewa.

“Mun gamsu ƙwarai da gaske a tsawon waɗannan shekaru biyar na gudanar da aikin gina makarantar. Mun samu cikakken haɗin kai da kyakkyawan yanayi na tuntuɓar juna tsakaninmu da hukumomin kula da gine-gine da na kiwon lafiya da kuma ´yan sanda a tsawon wannan lokaci. Yanzu haka tattaunawar da muke yi ta kai ƙololuwarta inda muke shawartawa da shugabannin birnin Berlin. An karɓe mu da hannu bi-biyu musamman daga ɓangaren hukuma.”

To sai dai duk da haka da akwai wasu mutane dake adawa da kafa irin wannan makaranta a saboda haka yake da muhimmanci a shiga tattaunawa da sauran ƙungiyoyin jama´a daban daban, inji Alexander Weiger. Yanzu haka dai an shirya gudanar da wani taron ƙarawa juna sani game da aƙidar sufaye a cikin watan Mayu. A irin waɗannan taruka za a riƙa yin waƙoƙi da kaɗe-kaɗe domin janyo hankula maƙwabta.

Cibiyar Buhara ta birnin Berlin ita ke ɗaukar nauyin tafiyar da wannan makaranta ta Islamiya. Membobinta su kimanin 300 yawanci daga ƙasar Turkiya, musulmai ne ´yan sunni waɗanda ke girmama alaƙarsu da masu aƙidar sufaye. Sunan wannan cibiya ya samo asali ne daga yankin da wanda ya kafa ta kuma mai wata makarantar sufaye ya fito, wato Buhara dake a ƙasar Usbekistan.

Dole sai an gabatarwa hukumar gudanarwa ta makarantu a Jamus manhajar koyarwa ta makarantar ta Buhara kafin a yi amfani da ita. Kuma hukumar ce za ta riƙa sa ido akan ayyukan makarantar. Cibiyar ta Buhara ta na ƙarƙashin uwar ƙungiyar Semekand dake a birnin Berlin, kuma membobinta sun shafe shekaru masu yawa suna gudanar da ayyukan taimakawa jama´a kamar ga yara da matasa, kana kuma suna ba da babbar gudunmawa a tattaunawa da ake tsakanin addinai daban daban.

Tun kimanin shekaru 30 da suka wuce aka kafa tarayyar Musulmai a Berlin wato IFB wadda ke tafiyar da masallatai 12 a babban birnin na tarayyar Jamus. Tarayyar ta IFB ta duƙaufa wajen kyautata zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka tsakanin musulmai da sauran al´umar wannan ƙasa. Shugabanta Altin Fazli ya bayyana kafa wannan cibiyar ba da ilimi ga matasan muslimin a matsayin wani mataki akan turbar da ta dace.

“Ina ganin ɗaliban wannan makarantar bayan sun sauke karatu, za su ba da gagarumar gudunmawa wajen yiwa jama´a aiki, kuma ta haka za a kawad da wariya da kuma kyamar da ake nunawa musulmai da addinin musulunci a tsakanin al´umar Jamus. Limami na matsayin abin koyi ga jama´a. Abin nufi shi ne wannan makarantar za ta horas da limaman domin su kasance abin koyi ba ma kawai a matsayin masu ba da ilimi ba a´a har da ma yaɗa kyawawan al´adu.”

Yildirim wani matashi ne daga birnin Dortmund a nan Jamus wanda iyayensa suka yi ƙaura daga Turkiya ya ce yana ɗokin fara karatunsa a makarantar ta horas da limamai a Berlin. A gun bukin buɗe makarantar Yildirim yayi amsa tambaya ko da son ransa ya zaɓi wannan fanni.

“Ni na zaɓan ma kaina. Kasancewar mahaifi mai zuwa masallaci ne a kullum a Dortmund, shi ya samo min bayani game da cibiyar ta Buhara. Kuma ni kaina mai bin dokokin addini ne amma ba mai matsanancin ra´ayi ba. Alal misali ina zuwa sallar juma´a kuma tun ina yaro ƙarami nake sha´awar addinin na musulunci.”

Kafin ya fara karatu a wannan makaranta Yildirim bai san birnin Berlin ba, to amma yanzu ya san muhimman wurare a birnin. Shin ko yaya yake tunanin aikinsa bayan ya kammala samun horon a wannan makaranta, Yildirim cewa yayi.

“Gaskiya zan yi limaci ne ko dai a wata cibiyar yaɗa al´adu ko kuma a wani masallaci a garin Dortmund, inda ake da buƙatar samun limami wanda ya iya harshen Jamusanci. Su ma Jamusawa dake zuwa masallaci za su ji daɗi idan aka yi huɗuba a cikin harshensu. Saboda haka na ke wannan makaranta.

Mawallafi: Sabine Ripperger / Mohammad Awal

Edita: Yahouza Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin