Sabuwar dangantakar Rasha da Turkiya | Labarai | DW | 09.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar dangantakar Rasha da Turkiya

A ziyararsa da ke zama ta farko tun bayan yunkurin juyin mulki da ya gaza nasara Shugaba Recep Tayyip Erdogan zai gana da Shugaba Vladimir Putin a St Petersburg a ranar Talatan nan.

Russland Recep Tayyip Erdogan und Wladimir Putin G-20 Türkei 2015

Shugaba Erdogan da Shugaba Putin

Kafin dai tafiyar ta Shugaba Erdogan ya bayyana cewa wannan ziyara tasa ita ce mataki na gaba a bude sabuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Shugaban na Turkiya ya ce ya na so su sake bude sabon shafi a dangantaka da ke tsakanin kasashensu ta fannin tsaro da tattalin arziki da ci gaban al'adu.

Dangantaka dai tsakanin kasar ta Turkiya da kawayenta na Turai da Amirka ta yi tsami bayan da kasar ta tasamma al'ummarta da kame-kame da gallazawa da sunan zagin wasu da kitsa juyin mulki da bai samu nasara ba.

Su ma dai Rasha da Turkiya an nuna 'yar yatsa bayan da Turkiya ta kakkabo wani jirgin Rasha a kan iyaka da Siriya a watan Nuwambar bara.