Sabon wa′adi na rajistar masu zabe a Nijar | Siyasa | DW | 16.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon wa'adi na rajistar masu zabe a Nijar

Karo na uku ke nan da hukumar kula da rajistar ke kara wa'adi, sakamakon kura-kurai, yanzu ana sa ran kammala rajistan ranar25 ga watan Nuwamba.

Hukumar CEFEB mai aikin rijistar sunayen masu zabe ta sake dibarwa kanta wani sabon wa'adi na damka kundin sunayen masu zaben a hannun hukuma, biyo bayan kammala yiwa kundin gyaran fuska bisa la'akari da kura-kuran da ya fuskanta. A karon farko dai hukumar ta yarda da cewar kundin na tattare da kura kurai kuma ta yi alwashin gyarasu kafin nan da 22 ga wannan watan na Nuwamba. Sabon wa'adin da hukumar ta CEFEB ta dibarwa kanta na zuwa ne 'yan kwanaki kalilan bayan wata sanarwa da kawancen jam'iyyun adawa suka fitar na yin tir da Allah wadarai da sabon kundin, tare da yin watsi da shi bisa kura-kuran da suka ce kundin ya tanada wanda da ke iya zama fitin a lokutan zabe.


Ko baya ga jam'iyyun siyasar ma kundin ya sha kakkausar suka daga bangarori daban-daban da suka hada da kungiyoyin farar hula da ke zargin hukumar da yin sakaci wajen aikin mai matukar mahimmaci, da ke tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yayin zabe.

Da yawa sun amince da cewa akwai kura-kurai

Malam Salifou Rabiou, Kakakin kwamitin zartarwa ne na hukumar ta CEFEB ya kuma shaida mani da cewar kwamitin ya aminta da korafe-korafen dimbin kura-kuran da jama'a suka yi ta Magana a kai kuma sun dauki wa'adin sake gyarawa kundin fuska.


"Mu da kanmu mun lura da cewar akwai su kuma sun muna zafi kuma kura-kurai ne da muka lura da cewar mutanen mu na nan su ne musamman ma masu aikin rubuta sunayen sune suka yi kura-kuran yanzu babban gurinmu ranar 25 ga wannan watan ne muke son mu bayar da aikin nan fatarmu kenan, - a samu a kammala aikin ".

To a baya kunsha bayar da ire iren wa'adin nan har sau biyu baka ganin wata kila wannnan karon ma ba zaku iya cika wa'adin ba gain irin kura kurran da kundin ya kumsa?

"Shi buri ga zuciya shi ke cika guri kuma sai Allah"

Wähler vor Wahllokal in Tahoua Niger

Sahihancin Kundin masu zabe zai tabbatar da zabe mai tsabta

To yaya kawancen jam'iyyun adawa suka ji da sabon wa'adin da hukumar ta CEFEB ta dibarwa kanta don gabatar da sabon kundin zaben? Tambayar kenan da na yi wa Mourtala Alhaji Mamouda sakataren yada labarum jam'iyyar MNSD nasara mai adawa.


"Dole ne saboda kun ji ai kura-kuran da ke da akwai a ciki sun wuce kima manyan kura-kurai ne da ba'a taba gainsu ba kuma Allah da ikonsa a da suna cewar babu wadannan kura-kuran a yanzu kuma sun yarda da cewar akwai su, to kenan yau talakawan Nijer da duk mutanen duniya kowa ya san abinda muke fadi ba karya ba ne muna da hujja kuma ba abinda gwamnati take cewa bane wai mu bamu son zuwa zabe, kage ne kawai muke kowa ya san kenan da hujja abinda duk muke fadi, a yanzu alkawari ne suka dauka kenan sai munga abinda zai biyo daga baya ai kamar da a ciki sai an ga fitowar shi kurum".


Martanin hukumar CEFEB

Na yi tattaki dai har izuwa cibiyar da hukumar ta CEFEB ta kebe inda take aikin gyara kura-kuran da tace ta lura na kuma ci karo da wasu da suka fito daga jihohin kasar dauke da kura kuran da suka lura kuma hukumar ta ke aikin gyarawa.


"Suna na Abdullahi Mahamman kakakin hukumar CEFEB daga Zinder cikin kura- kuran da muka samu sun hada da mutanen da sunayensu ya fito a karamar hukumar da ba a nan ya kamata ya fito ba hakan kuma duk wasu kura kurran da suka fito mun dawo dasu a yanzu muna nan muna gyara kamar wadanda sunayensu aka sauya su kana yanzu da nike maka Magana daga cikin karamar hukuma 55 mun samu kimanin biyar da muka gyara."

"Suna na Malam Masa'oudou ne daga jihar Tillaberi Alal hakika mun samu kamar kura-kurai da yawa da suka hada da kamar runfunan zabe da yawa ko kuwa mu samu mutanen da suka yi yawa fiye da kima har su wuce yanda doka ta bada ko kuwa suka yo kasa hakan kuwa da samun sunayen muataen wagga gunduma zuwa waccan gunduma a takaice irin kura kurran da muka samu kenan."


Yanzu hakan dai hankalin yan kasar ta Nijer ya karkata akan sabon wa'adin na hukumar cefeb da irin yanda za'a kaya a baya idan hart a kare kundin ta damka shi ga hukumomin kasar ganin irin yanda a baya a ka sha cece-kuce kansa tare da zargin tabka magudi.

Sauti da bidiyo akan labarin