Sabon tsarin tsaron kan iyaka a EU | Labarai | DW | 22.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon tsarin tsaron kan iyaka a EU

Kasashen kungiyar Tarayyar Turai wato EU sun amince da sabon tsarin tsaron kan iyakokin kasashen na bai daya.

Shirin tsaron kann iyaka na kungiyar EU

Shirin tsaron kann iyaka na kungiyar EU

Sabon shirin wanda zai dora a kan shirin tsaron gabar tekun kan iyakokin kasashen na Frontex, zai fara aiki ne daga lokacin bazara na wannan shekara, da nufin kare kan iyakokin kasashen na EU. A karkashin shirin dai za a dauki ma'aikata kimanin 1000 da kuma masu tsaron kan iyakokin kasashen 1 500. Wannan sabuwar yarjejeniya dai za a fara aiki da ita da zarar majalisar ministocin Tarayyar Turan ta amince da shi.