Sabon shirin horas da malamai a Kano | Zamantakewa | DW | 13.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Sabon shirin horas da malamai a Kano

A wani mataki na samar da ilmi mai inganci gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta tura dubban malaman firamare manyan makarantun ilmi don su nakalci dubarun koyarwa.

Kimanin malaman makarantun firamare 26000 ne gwamnatin jihar ta Kano da ke arewacin Tarayyar Najeriya ta tura manyan makarantun ilmi mai zurfi na jihar don su nakalci dabarun koyarwa ta yadda matsayin ilmin firamare a jihar zai kara inganta.

Wannan mataki kuwa ya biyo bayan manufar da gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta tsayar ne cewa sai malaman da suka mallaki takardar shedar koyarwa ta NCE ne kadai za su koyar a makarantun firamare.

Wadannan malaman makarantun firamare na Kano sun kasu gida uku kama daga kan wadanda matsayin ilminsu bai wuce na sakandare ba sai masu diploma da kuma masu digiri da babbar diploma ta kasa amma kuma a dukkan karance karancensu na ilmi a baya babu darasin ilmi wanda da shi ne malami zai nakalci dabarun koyarwa.

Raunin hanyoyin koyarwa sakamakon karancin darasin ilmi

Rashin hadawa da darasin ilmin ne kuwa yake kawo raunin dabarun koyarwar da ake bukata da ma sauran matsaloli na koyarwa.

Malam Abubakar Abdullahi Bichi shi ne shugaban da ke kula da shirin a Kwalejin ilmi ta Tarayya da ke Kano. Ya yi karin haske a kan sauran matsalolin malaman kamar yadda suka lura da su a farkon karatunsu.

"Na farko dai yawancinsu ba su da wayewa. Wasunsu sun zo daga karkara ne kuma ba sa mu'amala da mutane dabam-dabam. Da yawa ya sa wasunsu ba su da wayewa ta gogayya wadda kuma ana bukatarta ya zamanto malami ya zamo wayayye kuma mai gogayya don ya iya cudanya da sauran al'umma yadda ya kamata don ya isar da sakon da ake bukata."

Kwalliya ta fara mayar da kudin sabulu

A yanzu dai an dauki tsawon lokaci ana gudanar da wannan shiri wanda ya zo daidai da lokacin hutun dalibai wanda a cewar Malam Mujtaba Ahmad daya daga cikin malaman da ke amfana da shirin tun daga yanzu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.

"Tun daga yanzu da muka fara shirin satin nan kwaya biyar, muka fara ganin ci gaba, mun fara samun gamsuwa, mun fara yarda a kan cewa lalle nan gaba za mu sami kyakkyawar tarbiyyar koyarwa ta makarantun firamare."

Malaman makarantun na firamare za su yi shekaru daga biyu har zuwa biyar suna wannan horo na sanin makamar aiki kasancewar sai a lokutan hutu makarantunsu ne za su ci gaba da yinsa. Tuni har wasunsu sun fara nuna sha'awar yin digiri da zarar sun kammala wannan.

Mawallafi: Abdulrahman Kabir
Edita: Mohammad Nasiru Awal