Sabon salo a yaki da ta′addanci a Najeriya | Siyasa | DW | 14.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon salo a yaki da ta'addanci a Najeriya

An bayyana sunayen wadanda suka kai hare-hare a Kuje da Nyanya a Abuja ranar biyu ga watan Oktoba abin da ya sanya sake duba a yaki da ta'addanci a kasar.

Nigeria Bombenanschlag in Abuja

Wurin da aka kai hari a Abuja Najeriya

Sannu a hankali dai ana ci gaba da ganin sauyi daga yadda jami'an tsaron Najeriyar ke tunkarar masu kai hare-hare na ta'adanci irin na dasa bama-bamai a cikin al'umma musamman a manyan biranen kasar irin na Abuja. Domin kuwa cikin ‘yan kwanaki kalilan da suka kai tagwayen hare-hare a unguwanin Kuje da Nyanya da ke Abuja da suka sake tunawa birnin mugun hali na tashin hankalin da ya shiga a watanin baya ‘yan sandan Najeriyar sun sanar da kame mutanen da suka kitsa harin har ma da wasu kayayyaki na hada bam da ‘yan sadan suka ce suna shirin kai wani sabon harin ne.

Sifeto Janar na rundunar ‘yan sandan Najeriyar Solomon Arase ya bayyana mutanen da aka kama.

Anschlag in Abuja, Nigeria

Al'umma cikin dimuwa bayan kai harin ta'addanci

"Wadanda aka kame sun hada da Abdul'Azeez mai shekaru 27 daga jihar Kogi da kuma Isiyaku mai shekaru 25 shi ma daga jihar Kogi, an gano wasu kayayyaki a wajansu wadanda suka hada da abubuwan da ke fashewa har 12 da kaya masu yawa da ake hada bama-baman da ake kai hari da su. Ku sani cewa samun yanci na daga sa ido da jajircewa''.

Ganin cewa a yanzu ana samun wannan sauyi daga yanayin kai hari aji shiru ya zuwa inda cikin kankanin lokaci ake samun kame wadanda ake zargi ya sanya nuna sambarka. To sai dai ga Mallam Kabiru Adamu masani a fanin tsaro ya ce ci-gaba ne amma akwai fanin da ya kamata jami'an tsaron su kyautata don ganin tasirin matakin.

Abuja Anschlag 14.04.2014

Jami'ai na nazari bayan harin bam a tashar motoci

" Muhimmin abu shi ne a hukunta wanda ake zargi, amma in aka duba a baya sai kaga an kama mai laifin, amma an kasa hukunta shi. Kamawa yana da kyau amma nuna shaidar cewa shi ya aikata yana da muhimmanci. Ya kamata a dauki matakai na tsaron cikin gida wanda banga ana dauka ba, inda za'a taimakawa jama'a wanda su ake kaiwa hari zai taimaka".

To sai dai duk da wannan haske da ake hange a fanin yaki da aiyyukan ta'adancin bukatar bakado wadanda ke daukan nauyin mutanen da ake zargin suna kai hare-haren na kara bayyana, abin da ya sanya mataimakin sakataren jamiyyar PDP mai adawa Barister Jallo bayyana cewa lokaci ya yi da za'a bar boye-boye.

Ga al'ummar Najeriyar musamman wadanda ke yankin Arewaci da wannan matsala tafi shafa, na masu sa ido a kan wa'adin da sojoji suka dibawa kansu na kawo karshen matsalar nan da watan Disamba musamman hare-hare da ke dalilin aika wa da su lahira a wuraren gudanar da harkokinsu.

Sauti da bidiyo akan labarin