Sabon harin kunar bakin wake a Potiskum | Labarai | DW | 18.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon harin kunar bakin wake a Potiskum

Dan kunar bakin waken ya hallaka mutane biyar wasu kuma sun jikata a wata mahada da ke tara jama’a a Potiskum mai nisan km100 daga Damaturu fadar gwamnatin Yobe.

Wata majiya ta asibitin garin na Potiskum, ta tabbatar wa wakilin mu namu Amin Suleymane Mohammed cewa, an kai gawawaki biyar ciki har da ta dan kunar bakin waken, inda wasu mutane kusan 50 da suka samu raunuka, ke samun kulawar likitoci. Shaidun gani da ido sun bayana wa wakilin mu na Gombe ta wayar tarho cewa dan kunar bakin waken ya isa wurin cikin wata karamar mota wacce bata da lamba da musalin karfe 10 na safe, inda ya tada Bam din.

Garin Potiskum dai na fama da tashin bama-bamai inda ko da a makon da ya gabata wasu tagwayen hare-hare sun hakkala jama'a a wata kasuwar da ke wannan gari.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba