Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Damaturu babban birnin Jihar Yobe kana daya daga cikin wuraren da ya fuskanci rikicin Boko Haram.
Birnin da wasu sassan jihar sun fuskanci rikice-rikice na Boko Haram da hare-hare a makarantu, abin da ya janyo mutuwar mutane da dama.
Wani hadari mai muni da ya auku a yankin arewa maso gabashin Najeriya ya salwantar da gomman rayuka a wannan Talata. Hadari ne da ya hada wasu motoci biyu.
A Najeriya an shiga rudani da damuwa bayan da sojoji sun rufe hanyar daya tilo da ta saura wacce ake shiga Maiduguri daga wasu wurare saboda kaddamar da wasu hare-hare kan mayakan Boko Haram da ke yankunan.
A’ishatu Aje Gwaigwai matashiya ce da yi watsi da digiri ta shiga sana’ar dafa abinci da dinka kayan kawa na zamani a Damaturu da ke jihar Yobe, Najeriya.
Mazauana kauyukan da ke kan hanyar Damaturu Zuwa Maiduguri sun shiga rudani bayan da mayakan bangaren Boko Haram wato ISWAP suka yi garkuwa da wasu masu aikin jin kai na Red Cross da kuma wani jami’in Sojoji.
A cikin shirin za ku ji cewa wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hari a barikin sojojin Najeriya da ke kauyen Sasawa kilomita 27 da Damaturu
Da fari dai an tattara fulani ne da nufin za a yi musu wa'azi sai kawai aka ji tashin bam a tsakaninsu, abin da ya raunata da halaka mutane.
A cikin shirin za a ji an kai hari a Damaturu jihar Yobe Najeriya yayin da a kasar Ghana ake zargin shigar da baki cikin kundin masu zabe.
Wasu hare-haren bama-bamai na kunar bakin wake da aka Kai a jihohin Yobe da Gombe da ke Tarayyar Najeriya a jajiberin Sallah da kuma ranar Sallah, sun kara jefa al'ummar kasar cikin alhini da fargaba.
Wasu tagwayen bama-bamai sun tashi a Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe a wani Masallacin Idi da ke Layin Gwange daura da tsohuwar sakatariyar gwamnatin jihar ta Yobe.
Wani bam ya tashi a wata tashar mota mai cinkoson jama'a a garin Damaturu a yabkin Arewa maso gabashin Najeriya a yau Lahadi. Harin ya ritsa da mutane da dama.
Dan kunar bakin waken ya hallaka mutane biyar wasu kuma sun jikata a wata mahada da ke tara jama’a a Potiskum mai nisan km100 daga Damaturu fadar gwamnatin Yobe.
Bayan hare-haren da al'ummar Damaturu ta wayi gari da su, mahukuntan jihar sun ce jami'an tsaro sun fatattaki maharan kuma kura ta lafa yanzu.
Wadannan hare-haren sun afku ne a kasuwar Maiduguri, inda aka kai wasu hare-haren masu kama da su a makon guda da ya gabata.
'Yan bindiga da ake zaton ‘yan Kungiyar Boko Haram ne sun afkawa garin Damaturu, inda ake jin karar fashewar bindigogi da kuma abubuwa dake kama da bama-bamai.
Hukumomi a jihar Yobe sun kafa dokar hana fita ba dare ba rana a Damaturu, babban birnin jihar bayan wani sabon tashin hankali da ya barke.
Aƙalla mutane shida sun rasu a tashin-tashina da suka auku a birane uku dake arewa maso gabacin Najeriya.