Sabon harin Boko Haram a Najeriya | Labarai | DW | 11.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon harin Boko Haram a Najeriya

Wani sabon hari da mayakan Boko Haram suka kai a kauyen Kamuya da ke yankin karamar hukumar Biu a jihar Borno, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 14 tare da jikkata wasu da dama.

Sojoji na kokarin kawo karshen hare-haren Boko Haram a Najeriya

Sojoji na kokarin kawo karshen hare-haren Boko Haram a Najeriya

Mazauna kauyen wanda suka tsira daga wannan hari da suka isa garin Biu sun bayyana cewa 'yan kungiyar sun shiga kauyen ne a kan kekuna wasu kuma da kafa cikin dare, inda suka yanka mutane bakwai suka kuma harbe wasu guda bakwai har lahira. Sun kuma kone daukacin gidajen da ke kauyen wanda ke zama garin mahaifiyar babban hafsan tsaron Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai. Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun nunar da cewa babu wani dauki da sojojin suka kai wannan garin mai nisan kilomita 10 daga Buratai mahaifar babban hafsan Sojojin kasar. Ana ci gaba da samun hare-hare daga mayakan Boko Haram a dai-dai lokacin da wa'adin da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya dibar wa sojojin kasar na su murkushe kungiyar ke cika.