Sabon hari a Goza ya hallaka mutane | Labarai | DW | 06.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon hari a Goza ya hallaka mutane

Rahotanni daga garin Goza a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun kai harin da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane masu yawa.

Wani da ya tsira daga wannan hari ya shaida wa wakilin mu na Gombe Al-Amin Suleiman Mohamed cewa tun da misalin karfe hudu na asubahin wannan Laraba 'yan bindigar suka shiga garin tare da yin harbin kan mai uwa da wabi da kuma yanka mutane da kona gonaki da gidaje da sauran gine-gine. Kawo yanzu dai babu alkaluma na adadin wadanda suka mutu a wannan harin sai dai wani shaidan gani da ido da ya ce ba ya so a bayyana sunansa ya tabbatar da cewa mutane sama da 100 sun mutu haka nan ma yawancin jama'ar garin sun tsere. Shima wani bawan Allah da ya tsira wanda a yanzu haka ya isa jihar Adamawa ya shaidawa wakilin namu ta wayar tarho cewa 'yan bindigar sun tarwatsa wannan gari na Goza yayinda jami'an tsaro da ke garin suka tsere.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal