Sabon gumurzu a kasar Syria | Labarai | DW | 17.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon gumurzu a kasar Syria

Fada ya sake kazanta tsakanin mayakan tawaye da ke da goyon bayan gwamnatin Turkiyya da kuma mayakan Kurdawa bayan arangama tsakanin bangarorin biyu a yankin arewa maso yammacin kasar Syria.

Rahotanni sun ce an fafata tsakanin bangarorin biyu ne kusa da wani sansanin mayakan saman Syria a kauyen An-Dakna da ke arewacin birnin Aleppo.

Kungiyar sa ido da kare hakkin jama'a a Syria ta Syrian Observatory for Human Rights mai mazauni a Birtaniya, ta ce dakarun kasar Turkiya sun ja daga a wasu wurare da ke kewayen yankin da rikici ya faru a wannan Litinin.

Wasu sojojin gwamnatin Syriar sun ce an halaka wasu daga cikin 'yan tawayen da ke da goyon bayan kasa Turkiyya a arangamar.