Sabon fata a rikicin kasar Ukraine | Labarai | DW | 27.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon fata a rikicin kasar Ukraine

Bangarorin da ke yakar juna a kasar Ukraine sun ce za su dakatar da karya ka'idojin yarjejeniyar sulhun da suka cimma a tsakaninsu a birnin Minsk.

Rikicin Ukraine da kokarin tsagaita wuta

Rikicin Ukraine da kokarin tsagaita wuta

Kungiyar tsaro da hadin kan Turai OSCE ce ta sanar da hakan, inda ta ce bangaren gwamnatin Ukraine din da kuma 'yan awaren gabashin kasar da ke goyon bayan Rasha sun amince su fara mutunta yarjejeniyar sulhun yadda ya kamata daga ranar daya ga watan Satumba mai zuwa, ranar da makarantun kasar za su fara zangon karatunsu na wannan shekara. Kawo yanzu dai akwai manyan makamai na duka bangarorin biyu a filin daga wadanda ba a janyesu ba, duk kuwa da cewa yarjejeniyar da suka cimma a birnin Minsk din a watan Fabarairun da ya gabata ta tanadi hakan.