Sabbin shugaban Turai na shirin fara aiki | Labarai | DW | 22.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin shugaban Turai na shirin fara aiki

Majalisar Turai ta amince da nadin manyan jami'an hukumar ta Turai

Majalisar dokokin kungiyar Tarayyar Turai ta amince da kwamishinonin kungiyar da za si yi aikin da sabon Shugaban hukumar Jean-Claude Juncker, abin da ke tabbatar da fara akin sabon babban jami'in da tawogarsa ranar daya ga watan gobe na Nowamba.

Majalisar da ke zama a birnin Strabourg na kasar Faransa ta amince da kwamishinonin a wannan Laraba, inda 'yan majalisa 423 suka kada kuri'ar amincewa, yayin 209 suka nuna rashin amincewa, sannan wasu 67 suka yi rowar kuri'unsu.

Yanzu haka kasar Italiya take rike da shugabancin watanni shida da ake karba-karba na kungiyar ta Tarayyar Turai.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu