1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Sabbin hare-haren Rasha a Ukraine sun salwantar da rayuka

May 26, 2024

Wasu hare.haren boma-bomai da Rasha ta kai kan wajen hada-hadar jama'a, sun haddasa asarar rayuka a gabashin Ukraine. Hukumomi sun ce sama da mutum 100 ke a wajen.

https://p.dw.com/p/4gI0h
Hoto: Andrii Marienko/AP Photo/picture alliance

Rasha ta kai wasu munanan hare-hare ta sama a yankin Kharkiv da ake arewa maso gabashin kasar Ukraine, inda akalla mutum shida suka rasa rayukansu.

Hukumomi a yankin sun ce akwai wasu mutum 40 da su kuma suka jikkata a hare-haren da suka yi ta'adi a wani rukunin shaguna da ake kira DIY.

Magajin garin yankin ya ce akalla akwai mutane 120 wadanda ke a cikin shagunan a lokacin da lamarin ya faru.

Hare-haren da ke na boma-bomai, sun haddasa tashin wuta nan take a wajen.

Tun da farko dai Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar ta Ukraine ya wallafa a shafinsa na zumunta cewa akwai yiwuwar mutum 200 ne abin zai iya shafa a shagunan lokacin hari na farko.