Sabbin hare-hare a Maiduguri | Labarai | DW | 01.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin hare-hare a Maiduguri

Wadannan hare-haren sun afku ne a kasuwar Maiduguri, inda aka kai wasu hare-haren masu kama da su a makon guda da ya gabata.

Rahotanni daga jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, na cewa an kai wasu tagwayen hare-hare a wata kasuwa dake birnin Maiduguri, abin da ke zuwa mako guda bayan da wata 'yar kunar bakin wake, ta kai harin da ya hallaka akalla mutane 45 a wannan kasuwar.

Wani Ahmad Sanusi wani wanda ya shaida yadda harin ya afku ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, wata mata ce mai kimanin shekaru 40 na haihuwa, ta yi yunkurin zuwa wajen da ake sayar da kaji a kasuwar, sai kuwa 'yan bangan da ke tabbatar da tsaro a wajen suka dakatar da ita, daga nan ne kuwa, ta tayar da bam din da ke a jikinta.

Ya zuwa yanzu dai, ba a kaiga tantance adadin mutanen da suka halaka ko suka jikkata sakamakon wannan kunar bakin waken na Maiduguri a yau ba.