Sabanin ra′ayi kan yakar kungiyar IS | Siyasa | DW | 11.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabanin ra'ayi kan yakar kungiyar IS

Shirin gwamnatin Amirka na murkushe kungiyar IS da ke fafutukar kafa daular Islama a Yankin Gabas ta Tsakiya, ya janyo maida martani daban-daban daga ciki da wajen kasarsa.

Jawabin da shugaban Amirka Barack Obama ya yi dangane da shirin gwamnatinsa na yakar 'yan kungiyar ta IS da ke kokarin kafa daular musulunci a kasar Iraki da Siriya ya sanya jama'a daga bangarori daban-daban na duniya tofa albarkacin bakunansu dangane da dacewar shiga wannan yakin ko akasin haka.

Matakan da gwamnatin Amirkan ta ce za ta dauka dai sun hada kai hari ta sama, da horas da dakarun gwamnatin Iraki da na Kurdawa ta yadda hare-haren da za'a kai ta sama za su taimakawa sojojin wajen kutsawa zuwa muhimman yankunan da kungiyar ta ke, sannan kuma za su cigaba da kai tallafi domin kare rayukan mutanen da ke rayuwa a wadannan yankunan musamman Kiristoci da sauran tsiraru.

Obama - Rede an die Nation

Gwamnatin Amirka ta lashi takobin ganin bayan kungiyar IS

Babu shakka mazauna Iraki da dama sun karbi wannan jawabi cikin farin ciki, kuma wannan ya bayyana a irin tarbar da aka yi wa sakataren kula da harkokin wajen Amirkan John Kerry, wanda a yanzu haka ya ke ziyara a Saudiyya, inda zai gana da shugabanin kasashen Larabawan domin samun goyon baya wa kudurin shugaban kasar na sa a yankin Gulf

Ayad al-Milhani marubuci kuma mai sharhi kan lamura a Bagadaza ya ce ''da Shugaba Baraack Obama ya bayyana matakansa na murkushe kungiyar IS, mun fahimci cewa duniya ta fara la'akari da irin hatsarin da kungiyar IS ke da shi ga Amirka da Turai, saboda haka muna kallon wannan mataki na Obama a matsayin wani bangare na yakin da al'ummar kasa da kasa ke yi da ta'addanci, wanda ya mayar da hankali kan wannan kungiya, mai da'awar kafa daular Islama, waccce ta mamaye yawancin yankunan Iraki''

Islamischer Staat Propaganda

Kungiyar IS ta lashin takobin kafa daular Musulunci

Shi kuwa mai shiga tsakanin rikicin Siriya Steffan De Mistura wanda ke ziyara a Damascus a karon farko tun bayan da aka zabe shi ya cewa ya yi ''yaki da ta'addanci ba tare da an gaggauta daidaita tsarin siyasar kasar ba, zai janyo wani kalubalen tsaron na daban, saboda haka inganta rayuwar iyalan 'yan Siriya ya na kan gaba a manufofinmu, domin abubuwa biyun sun atafiya ne hannu da hannu

Ganin cewa tun bayan zaben Shugaba Obama ya nuna cewa shi ba shi da niyyar ya rika tura dakaru yaki kamar yadda gwamnatocin da suka gabace shi suka yi, ko me ya sa yanzu ake ganin sauyi duk da cewa ya ce ba zai tura dakarun yakin kasa ba, shin kungiyar ta ISIS babbar barazana ce ga Amirka? Jacob Zenn wani kwararre kan lamuran da suka shafi ta'addanci ya ce ''yan ta'adda za su iya amfani da fasfo dinsu su dawo gida su yi ta'adi ko kuma su tura wasu su zo su dana bama.bamai a sunan ramuwa, ga hare-haren da Amirkan za ta kai musu ta sama a Siriya da Irak"

To sai dai duk da ra'yoyi mabanbanta da ake cigaba da bayyanawa, a hannu guda hugaba Barack Obama ya jaddada cewa wannan matakin da kasarsa za ta dauka kan 'yan IS din zai banbanta da duk sauran irin shi da aka dauka a baya.

Sauti da bidiyo akan labarin