Ruwa ya ci sansanonin ′yan gudun hijira | Siyasa | DW | 06.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ruwa ya ci sansanonin 'yan gudun hijira

Amabaliyar ruwa ta barke a sansanonin ‘yan gudun hijira da suka tserewa hare-haren Kungiyar Boko Haram a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya tare da fargabar barkewar cututuka.

Nigeria Flüchtlingscamp in Maiduguri (picture-alliance/AP Photo/S. Alamba)

Daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira a Maiduguri Najeriya

Hukumomi a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya sun tabbatar da ibtila'in ambaliyar ruwa a wasu sansanonin 'yan gudun hijira da ke samun mafaka a jihar, inda suka bayyana shirin kai dauki ga 'yan gudun hijira.

Likitoci masu zaman kansu sun nuna fargabar barkewar cututuka sanadiyyar ambaliyar tare da jan hankalin hukumomin jihar Borno da su gagauta daukar matakai mafi sauki don kare al'umma. 

Wannan matsalar ta barkewar ambaiyar ruwa na zuwa ne a daidai lokacin da Kungiyar Boko Haram ta hallaka mutum fiye da 50 a kasa ga makwanni biyu ciki har da sojoji, a yayin da kungiyar ke kara zafafa hare-hare a wasu sassan jihohin Borno da Yobe lamarin da ke haddasa tserewar daruruwan mutane daga garuruwansu zuwa wuraren da su ke ganin tudun na tsira ne.