1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rohoto kan illar Boko Haram

Al-Amin Suleiman Mohammed/USUSeptember 22, 2016

Sabbin alkaluman da aka fitar sun nuna cewa sama da mutane miliyan 14 rikicin Boko Haram ya shafa a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya kuma sama da miliyan biyu ke cikin tsananin bukatar taimakon abinci.

https://p.dw.com/p/1K6on
Symbolbild Nigeria Bama Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

Rahoton da Kungiyoyin wato The 21st Century Wilberforce Initiative da Stefanus Foundation suka fitar, ya nuna cewa daga cikin wadan nan alkaluma akwai malaman makarantun Boko guda 611 da suka hallaka a rikin, wasu malamai dubu 19 suka rasa matsugun su, inda makarantu 1500 suka lalace abinda ya sa yara dubu 950 ba sa zuwa makaranta.

Haka kuma an sace mutane sama da dubu tare da tilasta yara da matasa dubu 10 shiga mayakan Kungiyar, da kuma lalata wuraren ibada na Musulmi da Kirinsta ko dai rushe su gaba daya ko kuma lalata su ta yadda ba za a iya amfani da su ba.

Dama dai alkaluaman da aka fitar da barnar da Kungiyoyin gwagwarmaya su ka yi, ya nuna cewa Kungiyar Boko Haram ta fi dukkanin sauran kungiyoyin hallaka jama’a bisa kididdiga na yawan wadan Kungiyoyi ke kai wa hare-hare tare da hallaka su.
A Disambar shekara ta 2015 alkaluma sun nuna cewa akwai wadanda rikicin Boko Haram ya raba da matsugunun su ya kai miliyan biyu da dubu 152 wanda ke zama na uku mafi girma a nahiyar Afirka, kuma na bakwai a fadin duniya.M'M

‘Yan gudun hijirar wadan da mafi yawan su suna zaune ba a sansanonin ‘yan gudun hijira ba, kuma suna cikin mawuyacin hali ba tare da samun tallafi da ya kamata ba. Kamar yadda Abubakar Mustapha Damboa wanda aka fi sani da Justice ya shaida wa DW.

Rahoton kungiyoyin agajin ma dai ya bayyana cewa abin takaici shi ne duk da dimbin matsalolin da al’ummar yankin suka shiga, babu cikakken aiki jin kai da ake gudanar da ya dore a shiyyar, haka kuma manyan kasashen duniya ba su maida hankali wajen tallafa al’ummar da ricikin ya shafa ba.

Dr Umar Adamu na Jami’ar jihar Gombe mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum a Najeriya, ya gaskata wannan matsayi na rashin samun taimako na rage wa wadanda abin ya shfa radadin da suke ciki.

Kungiyoyin fararen hula sun nemi hukumomi su fito da hanyoyin sake tsugunar da wadan nan bayin Allah, a kuma samar musu da yadda za su dogara da kan su kamar yadda Sani Adamu, kakakin gamayyar kungiyoyin fararen hula ya bayyana wa tashar DW.

Kungiyoyin da ke kula da ayyukan jin kai, sun nemi manyan kasashen duniya da su fara aikowa da kayan agaji zuwa ga wannan shiyya, wanda rikcin Boko haram ya dai-daita, wanda kuma ke fuskantar kalubalen sake farfadowa. Wannan rahoton kungiyoyin, ya zo ne a lokacin da , yanzu haka dai shugaba Muhammadu Buhari na halatan taro a kasar Amirka, inda ake saran zai nemi tallafion kasashen duniya kan agazawa mutanen da rikicin na Boko Haram ya shafa a Najeriya.