Rikicin Ukraine ya fara lafawa | Labarai | DW | 27.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Ukraine ya fara lafawa

An fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a gabashin Ukraine tsakanin gwamnati da 'yan aware masu goyon bayan Rasha

Bangarorin da ke rikici da juna a kasar Ukraine sun dauki gagarumin mataki na kawo karshen tashin hankalin gabashin kasar, inda suka bayyana fara janye manyan makamai. Cikin 'yan kwanakin da suka gabata an samu lafawar tashe-tashen hankula tsakanin gwamnatin Ukraine da 'yan aware, sai dai har yanzu akwai sauran zaman tankiya.

Ma'aikatar tsaron kasar ta yi gargadin cewa za ta fice daga cikin shirin janye makaman muddun 'yan aware suka kai farmaki kan dakarun kasar. Kasashen Jamus da Faransa sun nemi ganawar Kwamitin Sulhu na MDD a wannan Jumma'a, bisa rikicin na gabashin Ukraine da ake samun alamun fara aikin da yarjejeniyar tsagaita wuta.