Rikicin siyasa a ƙasar Pakistan | Siyasa | DW | 16.03.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin siyasa a ƙasar Pakistan

Gwamnatin Pakistan ta yi alƙawarin mayar da alƙalai da aka kora tare da dakatar da duk wani matsin lamba ga masu fafutukar kare haƙƙin bil Adama, tana mai miƙa wuya bayan zanga zanga da ta kusa yin kaca kaca da ƙasar

default

Zanga-zangar ´yan adawa a Pakistan

Bayan tattaunawa tsakaninsu da shugaba Ali Zardari da babban hafsan sojojin ƙasar, firaminista Yousuf Reza Gilani ya sanar da cewa za a maida alƙalin alƙalan ƙasar Iftikar Chaudry da sauran alkalai da aka saukar, za su kuma koma bakin aikinsu a ranar 21 ga wannan wata da muke ciki, bayan alƙalin alƙalai na yanzu ya yi ritaya.

Zardari ya samu kansa cikin matsin lamba ne daga ƙasashen yamma, cewa dole ya kawo ƙarshen sa in sa dake tsakaninsa da Nawaz Sharif, wanda ya yi kira ga talakawa da su ƙaddamar da zanga zanga na neman gwamnati ta mayar da alƙalan da Pervez Musharraf ya kora, saboda tsoron cewa zasu haramta masa sake tsayawa takara.

Tun da farko an shirya gudanar da wata babbar zanga zanga a yau Litinin, bayan zanga zangar jiya Lahadi inda Sharif ya yi watsi da ɗaurin talala da aka yi masa ya jagoranci zanga zangar wadda ta kusa wuce gona da iri .

Zanga zangar ta jiya mafi girma tun lokacin da rikici ya ɓarke makonni uku da suka shige ake ganin ta tsorata shugabannin ganin cewa zanga zanga irin haka ne ya tilasatawa tsohon shugaba Musharraf yin murabus a watan Agustan bara. Duk da dage dokar dai wasu lauyoyin sun baiyana shakkunsu ko zata tabbata ganin irin yadda aka saba karya alkawura a bangaren gwamnati.

"Bari dai mu tsaya mu ga abinda zai faru,sai mun ga Iftikar Chaudry zaune kan kujerarsa ta alkalin alkalai sannan ku tambaye ni."

Cikin jawabin nasa Gilani ya janye haramci kan gudanar da zanga zanga,yana mai baiwa hukumomin ƙasar umurnin sake dukkan masu zanga zanga da aka tsare.Haka kuma ya ce gwamnati ta yanke shawarar ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke na haramtawa Nawaz Sharif da ɗan uwansa Shahbaz Sharif tsayawa takara.

Imran na wata ƙaramar jam'iyar adawa yana ganin wannan abu dai wani ƙaramin juyin juya hali ne a fakaice.

"Abinda kuke ganin wani juyin juya hali ne a fakaice,na dokoki da kundin tsarin mulkin kasar, a karon farko a tarihin Pakistan wani alkali ya dage kai da fata kan bin kundin tsarin mulki a maimakon ,kan abinda yake dole ne a tsarin rayuwar jama'a."

Ƙasar Amurka dai ta yi maraba da wannan sanarwa da cewa wani mataki ne na kare wani mummunan rikici tare da sasanta tsakanin jama'ar ƙasar.

Saɓani tsakanin gwamnati da lauyoyi 'yan adawa da masu fafutukar kare demokraɗiya da suka neman a saki Chaudry sun yi barazanar ƙara rikita ƙasar mai ƙarfin nukiliya wadda kuma ke kan gaba wajen yaƙar 'yan Taliban da al-Qaeda.


Mawallafa: Sabina Matthay / Hauwa Abubakar Ajeje


Edita: Mohammad Awal