1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin cikin gida a jam'iyyar Labour

Uwais Abubakar Idris ZMA
April 6, 2023

Rigingimun cikin gida da ke fuskantar jamiyyar adawa ta Labour sun kara rincabewa inda wata kotu a Abuja ta hana shugabanta da wasu jami’anta ayyana kansu a matsayin shugabaninta.

https://p.dw.com/p/4PnHK
Nigeria | Präsidentschafts- und Parlamentswahlen
Peter Obi na jam'yyar LabourHoto: Patrick Meinhardt/AFP

Kasa da wata guda da kammala babban zaben Najeriya ne jam'iyyar adawa ta Labour da ta zo mataki na uku a babban zaben da aka yi duk da kasancewarta sabuwa, in aka kwatanta da sauran jam'iyyu biyu da suke gaba a kasar ta afka cikin rikicin cikin gida ne ,da ya sanya wasu tunkarar kotu da ta dakatar da shugaban jam'iyyar da sakatarensa Farouq Ibrahim da ma wasu jami'ai kan zargin sun yi amfani da takardun jabu na kotu suka sauya wasu ‘yan takarar jam'iyyar.

Kwararru na bayyana tsoron jam'iyyar duk da ban mamamki da ta yi a zaben shugaban Najeriyar da na ‘ya majalisu inda ta kai ga samun lashe zaben gwamna a jihar Abia, na iya fuskantara karkon kifi a fagen siyasar kasar, sanin yadda rikicin cikin gida ya yi wa sauran manyan jamiyyu a baya a kasar.

Wannan rikici na jamiyyar da ke faruwa a dai dai lokacin da dan takara neman shugaban kasarta Peter Obi ke kokari na yakice zargin da aka yi mashi da yace a yanzu yana fuskatar matsin lamba na ya tafi gudun hijira.

A yanzu ko ya koma babban kotun Najeriya inda can ne za'a tirje kasa a tsakanin shugabanin jamiyyar da kotu ta dakatar da su da wadanda suka dage cewa sai sun yi awon gaba da su a rikicin da yanzu aka fara shi.