Rikicin Rasha da Amirka ya kazanta | Labarai | DW | 31.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Rasha da Amirka ya kazanta

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya bayar da umurnin korar jami'an jakadancin Amirka akalla 700 daga Rasha, bayan kazantar dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu.

Dama dai ma'aikatar harkokin wajen Rashar ta ce za a rage jami'an na Amirka 455 ne gabanin sanarwar ta shugaba Putin, a lokacin da majalisar dattawan Amirka ta amince da tsananta batun takunkumi ga kasar.

Dangantaka tsakanin Amirka da Rasha dai ta yi zafi ne bayan zaben Amirka da aka yi a bara, zaben da ake zargin Rasha ta yi kutse a cikinsa.

Shugaba Putin ya kuma ce kada a yi tsammanin samun daidaito tsakanin Rasha da Amirka cikin dan karamin lokaci, yana mai kuma jaddada yiwuwar su ma su bullo wa Amirka da wani salo na takunkumin.