Rikicin jam′iyyar PDP yana kara tsananta | Siyasa | DW | 03.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin jam'iyyar PDP yana kara tsananta

A wani abun dake zaman alamu na kara lalacewar lamura a cikin PDP daya a cikin uku na 'yan majalisar dattawan Najeriyar daga PDP sun bayyana goyon bayan ga sabuwar PDP mai neman sauyi.

Foto: DW-Korrespondent Ubale Musa, 26.6.2013 in Abuja

.

Sannu a hankali dai al'amura na kara lalacewa, kuma kowa yana gane hanyar gidan iyayensa a cikin jam'iyyar PDP da yanzu haka ke ikirarin kokarin sulhunta tsakanin ‘ya'yanta, amma kuma kan na ‘ya'yan na ta ke kara darewa zuwa gida gida. Na baya baya dai na zaman wata sabuwar rabuwar da ta kunno kai a tsakanin ‘ya'yan jam'iyyar dake cikin majalisar dattawan kasar ta Najeriya. Akalla 22 a cikin senatocin jam'iyyar 67 ne dai suka ce suma sun bi, a kokarin tawayen da ya kai ga kafa sabuwar PDP, kuma ya ke barazana ga tasirin jam'iyyar a zabuka na gaba.

Kusan dukkanin senatocin jihohi bakwai dama wasu kari daga jihohin Taraba da Kebbi dai sun bi sahu wajen bayyana goyon bayansu ga sabon shugabancin jamiyyar dake kara karfi da samun gindin zama cikin sabon rikicin..

Nigerian Vice President Atiku Abubakar is interviewed by The Associated Press in Washington, Friday, Jan. 5, 2007. (AP Photo/Manuel Balce Ceneta) is interviewed by The Associated Press in Washington, Friday, Jan. 5, 2007. (AP Photo/Manuel Balce Ceneta)

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar

Ana dai kallon fadawar majalisar cikin rikicin a matsayin alamu na kara nisa da fatan sulhunta sabuwa da tsohuwar PDP da tuni shugabanninta suka sa kafa suka shure ci gaban tattaunawar sulhun da suka tsara komawa kai ranar Talata nan. Senator Abdulmumin Hassan dai na zaman daya daga cikin yan majalisar dattawan da suka rattaba hannu kan takardar amincewa da sabuwar PDP, kuma a fadarsa tura ce ta kaisu ga bango kuma aka kai karshen hakurinsu.

Fushi da shegiyar uwa ko kuma kokarin gyara ta dai daga dukkan alamu rikicin PDP na shirin komawa ga farfajiyar kotunan kasar, inda bangarorin biyu ke shirin gwada kwanji bayan rushewar kokarin sulhun cikin daka. Tuni da ‘ya'yan sabuwar PDP suka isa kotu suka kuma nemi wani alkali da ya haramta kujerar Bamanga Tukur da bangaren na Kawu Baraje yace ta gurbata, kuma tana shirin zama guba ga daukacin demokaradiyar Tarrayar Najeriyar. Matakin kuma da daga dukkan alamu ke shirin kara harzuka masu goya baya ga Bamangan da suka ce “hattara fa, makaho akwai rami da kaya a gabanka”, a cewar Senator Saidu Umar Kumo dake zaman mai baiwa shugaban PDP shawara ga harkoki na siyasa.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria

Rikicin jam'iyyar PDP ya fara isa majalisar dokokin Najeriya

Kokarin fadakar da magoya baya ko kuma kokarin ci da gumin su dai sabon rikicin dai ya kuma kama hanyar fitar da tsohon gyambon da ya dade yana wari a tsakanin rassa daban daban na jam'iyyar a jihohi. Alhaji Adamu Boy dai na zaman shugaban matasan PDP a jihar Yobe kuma a tunaninsa har yanzu taken jam'iyyar na zaman na asara maimakon sa'a a garesu.

Ranar Alhamis ne dai aka tsara bude offishin farko na sabuwar PDP kafin kaiwa ga bude masa rassa a daukacin jihohin kasar da Abuja.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin