1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Rikici ya lafa a jami'ar Yamai

Gazali Abdou Tasawa LMJ
September 21, 2022

Daliban jami'ar birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar da dama sun jikkata, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin tsofaffin mambobin kungiyar tsaron jami'ar wato CASO da kuma sababbin da aka zaba.

https://p.dw.com/p/4H9cJ
Nijar | Rikici | Yamai | Jami'a | Dalibai
Jami'ar Birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar NijarHoto: DW/Abdoulaye Mamane Amadou

Rikicin dai ya barke ne lokacin da tsofaffin mambobin kungiyar ta CASO suka kawo hari, da nufin kwatar abokinsu da sabuwar kungiyar ta CASO ta kama. Shekaru da dama kenan da dalibai a Jamhuriyar ta Nijar, suka fito da tsarin tsaron kansu, ta hanyar kafa kungiyar da suka kira CASO. Babbar kungiyar daliban jami'ar birnin na Yamai ta bayyana cewa da misalin karfe uku na daren Talatar da ta gabata ne, rikicin ya barke a wajen dakunan kwanan dalibai.

Nijar | Yamai | Dalibai | Zanga-zanga
Daliban birnin Yamai na zanga-zanga kan neman gyara a fannin karatunsuHoto: DW/Abdoulaye Mamane Amadou

Bayanai sun tabbatar da cewa rikicin ya barke ne lokacin da wani tsohon mamba na rundunar tsaron jami'ar, a cikin maye ya nemi hana motar daukar marasa lafiya fita da wani dalibin jami'ar mara lafiya zuwa babban asibitin jami'ar na CHU har sai da dalibin ya rasu. Wannan ta sanya shugabannin kungiyar tsaron jami'ar ta CASO suka kama tsohon mamba a kungiyar ta CASO suka tsare shi, inda bayan da labari ya kai ga sauran takwarorinsa sai suka yo takakkiya har cikin jami'ar. Tuni dai daliban suka ci gaba da karatu, koda yake har kawo yanzu ma'aikatar ilimi mai zurfi da ma gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar ba su ce komai kan wannan rikici da ya barke a jami'ar ta Yamai ba.