Shekaru biyu da kisan dalibin jami′a a Nijar | Siyasa | DW | 10.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru biyu da kisan dalibin jami'a a Nijar

Tunawa da dalibin da jami'an tsaro suka kashe na zuwa ne kwana daya bayan zanga-zanga da daliban makarantun sakandare na birnin Yamai suka gudanar inda suka yi ta kone-konen tayu da fashe-fashen kadarorin gwamnati.

Unruhen in Niger April 2014 (BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images)

Zanga-zangar dalibai ba bakuwa ba ce a Nijar kamar nan a 2014 a Niamey

Shekaru biyu kenan da zanga-zangar da ta jawo sanadin rai na wani dalibin jami'ar birnin Niamey a Jamhuriyar Nijar Mala Bagale. A wannan rana ta Laraba dalibai a Jamhuriyar ta Nijar dai sun koka da yadda mahukunta a kasar ba sa hukunta wadanda aka samu da laifi na kisan al'umma. Da dama dalibai a birnin na Niamey sun yi amfani da wannan rana ta tuni da shekaru biyu na kisan dalibin inda suka maimaita zama na makoki.

A cewar shugabannin dalibai da suka yi tattaki zuwa ga inda aka jibge dakarun tsaro a jami'ar Niamey sun karanta masu kasida da ke zama gargadi ga jami'an da suka ce ana amfani da su a ci zarafin dalibai.

Unruhen in Niger April 2014 (BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images)

Wata zanga-zanga kenan ta dalibai a Yamai a shekarar 2014

Wannan zaman makoki na daliban jami'a na zuwa ne kwana daya bayan wata kazamar zanga-zanga da daliban makarantun sakandare na birnin Yamai suka gudanar inda suka yi ta kone-konen tayu da fashe-fashen kadarorin gwamnati, yayin da suke neman biyan bukatu nasu daga bangaren gwamnati. Lamarin da ya fuskanci suka daga wasu 'yan kasar tare ma dora ayar tambaya kan dalillan da ke tura daliban yin barna a wasu lokuta na zanga-zangar neman wata bukata daga gwamnati.

Sauti da bidiyo akan labarin