1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 32 da kisan dalibai a Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
February 9, 2022

Daliban jami'ar Yamai fadar gwamnatin Nijar, sun gudanar da zanga-zangar shekara-shekara ta tunawa da ranar da jami'an tsaro suka yi wa wasu daliban jami'ar kisan gilla bayan bude musu wuta yayin wata zanga-zangar lumana

https://p.dw.com/p/46l1O
Nijar Zanga-zangar dalibai a Yamai
Shekaru 32 da kisan daliban jami'ar Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar NijarHoto: DW/Abdoulaye Mamane Amadou

Daiban dai sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne, domin neman inganta dimukuradiyya da harkar ilimi a kasar. Zanga-zangar ta bana da ke zama karo na 32 kan kisan gillar daliban uku da dubban daliban jami'ar birnin Yamai din suka gudanar, ta wakana cikin kwanciyar hankali da lumana. Daliban jami'ar da ma na makarantun sakandaren birnin na yin jerin gwano daga cikin jami'ar zuwa tsakiyar babbar gadar birnin, inda a nan ne jami'an tsaron suka bindige daliban masu zanga-zangar neman kafa dimukuradiyya a kasar. Sai dai Marie chitou daya daga cikin daliban ta ce shekaru 32 bayan gwagwarmayar tasu, har yanzu dimukuradiyyar Nijar din na son gyara.  Zanga-zangar shekara-shekarar ta daliban jami'ar Yamai din dai, na zaman zanga-zangar lumana mafi girma da ake shiryawa a kasar a kowace shekara. Daliban na share tsawon yini guda suna gabatar da makaloli kan ci-gaba ko akasin da aka samu a fannin dimukuradiyya da ma ingantuwar ilimi a kasar shekaru 32 bayan sadaukar da rayukan da 'yan uwansu uku suka yi.