Rikicin gwamnatin hadin kan kasar Nijar | Labarai | DW | 18.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin gwamnatin hadin kan kasar Nijar

Jam'iyyar PNDS Tarayyar mai mulkin Nijar ta yi kira ga jam'iyyar Moden Lumana Afirka da ta janye matsayin na dakatar da mambobinta daga shiga gwamnatin hadin kasa.

epa03142091 President of Niger, Mahamadou Issoufou delivers a speech during the opening ceremony of the 6th World water forum at Parc Chanot in Marseille, southern France, 12 March 2012. More than 1,000 high-level stakeholders are gathered in Marseille to share solutions to worldwide water problems and commit themselves to their implementation. EPA/GUILLAUME HORCAJUELO +++(c) dpa - Bildfunk+++

Niger Mahamadou Issoufou

Jamiyyar PNDS Tarraya mai mulki a Jamhuriyar Nijar ta yi kira ga abokiyar kawancenta wato jamiyyar Moden Lumana Afirka da ta janye matsayinta na dakatar da ministocinta daga cikin sabuwar gwamnatin hadin kasa da shugaba Isuhu Muhammadu ya girka a 'yan kwanakin da suka gabata.

Jam'iyyar dai ta yi kiran ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan Lahadin a birnin Yamai, fadar gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar bayan da ta kammala wani taron gaggawa da ta kira, daga bisani kuma ta kakakinta Malam Kalla Mutari ya yi jawabi ga manema labarai kan wannan batu.

Wannan kiran da jam'iyyar ta PNDS Tarayya din ta yi dai na zuwa ne kwana guda bayan da Moden Lumana Afirka ta bayyana cewar ministocin da aka bata a sabuwar gwamnatin sun gaza a saboda haka ta yanke shawarar dakatar da mambobinta daga kasancewa a cikin gwamnatin kamar dai yadda shugabanta wanda kuma ke zaman kakakin majalisar dokokin Nijar Hamma Ahmadou ya shaida.

Mawallafi: Gazali Abdou Tassawa
Edita: Umaru Aliyu