Rikicin gabashin Ukraine na kara rincabewa | Labarai | DW | 13.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin gabashin Ukraine na kara rincabewa

Mutane hudu sun hallaka a sabon rikicin da ya barke cikin yankin gabashin kasar Ukraine.

Rahotanni daga gabashin kasar Ukraine sun tabbatar da mutuwar fararen hula uku da soji daya yayin fafatawa da 'yan aware a wannan Talata.

Rundunar sojin kasar ta ce akwai wasu sojoji 10 da suka samu raunuka lokacin dauki ba dadin da 'yan awaren masu goyon bayan Rasha kusa da garin Donetsk.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal