Rikicin Boko Haram a Kamaru | Labarai | DW | 05.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Boko Haram a Kamaru

Wasu da ake zargin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a arewacin kasar Kamaru, inda suka hallaka mutane 19 suka sace wasu sama da 100.

A cewar kafen yada labaren kasar ta Kamaru, 'yan ta'addan sun kai harin ne a kauyen Tchakarmari da ke jihar Arewamai nisa. Harin da ya auku jiya Talata 04.08.2015, an ruwaito cewa bayan maharan sun kashe na kashewa, sun kuma yi awun gaba da mutane akalla 135. Sai dai kawo yanzu hukuma bata tabbatar da yawan alkaluman ba. Kasar Kamarun dai na cikin makobtan Najeriya da suka daura damarar ganin bayan kungiyar Boko Haram, cikin rundunar hadakar kasashe makobtan tabkin Chadi suke shirin girkawa.