Maroua ke zama hedikwatar Jihar Arewa mai Nisa a Kamaru, kuma daya daga cikin birane biyar da suka fi girma a wannan kasa.
Rikicin Boko Haram ya sa wannan birnin shiga cikin kanun labarai saboda hare-haren da ya fuskanta daga tsagerun Boko Haram. Amma Maroua ya yi fice ne a fannin aikin hannu irin jima da saka. Birnin ne ma cibiyar saka hular "Damanga".