Rikicin bashin Girka bai shafi Jamus ba | Siyasa | DW | 28.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin bashin Girka bai shafi Jamus ba

A daidai lokacin da EU ke shirin tattaunawa da Girka kan rikicin kudi da ya addabeta, gwamnatin tarayyar Jamus ta bayyana cewa tattalin arzikinta na kan kyakkyawar turba.

Gwamnatin ta Jamus ta fara hasashen cewa za ta iya samun bunkasar tattalin arziki na 1,3% a kafin karshen wannan shekara ta 2015. Sai dai kuma bayan zaman majalisar ministoci na wannan Larabar, ministan tattalin arzikin wannan kasa Siegmar Gabriel ya ce alkaluma sun nunar da cewa za su iya kaiwa kashi 1,5%. Wannan matsayin ba ya rasa nasaba da fargabar da kasashen Turai suke nunawa game da yaduwa da rikicin tattalin arzikin kasar Girka zai iya yi zuwa ga kasashen da ke amfani da takardar kudin Euro.

Sabuwar gwamnatin Girka ta Alexis Tsiprasta na nema a yafe wa kasar wani bangare na bashin da ake binta. Sai dai kasashe da dama suka ce ba za ta sabu ba ciki har da tarayyar Jamus.

Tsipras mit Giannis Varoufakis Archiv 2014

Firaministan Girka da ministan kudin kasar sun dahe kann bakarsu

Ministan kudinta Wolfgang Schäuble ya ce " harajin da Jamusawa suka biya ya taimaka wa Girka murmurewa daga halin da ta shiga."

Biliyan 278 na Euro ne kasashen Turai suka taimaka wa Girka da shi domin ta ceto tattalin arzikinta. A karshen watan Fabireru ne mataki na biyu na tsarin tallafa wa Girka zai zo karshe. Daga bisani ne ya kamata a shiga wani sabon babi na tattaunawa da nufin kara wa hukumomin Athens kudin da suke bukata don mayar da kasar kan kafafunta. Sai dai inda gizo ke saka shi ne sabuwar gwamnatin ta kudiri aniyar kin aiwatar da matakan tsuke bakin aljuhu, kamar yadda hukumomin da ke ta'ammali da kudi suka nemata da yi.

Ministan kudin Jamus Wolfgang Schäuble ya ce Girka ta kwana da sanin cewa Turai ta riga ta dauki matakan kare kanta daga irin wannan rikici. ya ce " Barazanar yiwuwar yaduwar rikicin tattalin arziki a kasashen da ke amfani da kudin Euro bai taka kara ya karya ba. Mun yi wa Allah godiya. Mun yi aikin tukuru a cikin shekaru biyar da suka gabata don cimma wannan matsaya."

Wolfgang Schäuble Eurogruppe Treffen in Brüssel 26.01.2015

Ministan kudin Jamus ya ce kasarsa ta taimawa Girka sosai

Shugaban rukunin kasashe da ke amfani da Euro Jeroen Dijsselbloem zai yi tattaki i zuwa Athens a ranar Jumma'a mai zuwa domin zama kan teburi guda da bangaren Girka don fahimtar juna kan duk al'amuran da suka shafi bashin da ake binta. Sabuwar gwamnatin ta Girka ta ce za ta yi iya kokarinta don kauce wa fito na fito tsakaninta da takwarorinta na Turai duk da banbancin manufofin tattalin arziki da ke tsakaninsu.

Sauti da bidiyo akan labarin