Rikici tsakanin Niger da kampanin Areva | Labarai | DW | 27.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici tsakanin Niger da kampanin Areva

Masu sauraro kamar yadda ƙila kuka riga ku ka sani, gwamnatin Jamhuriya Niger, ya yanke shawara kora shugaban kampanin Areva daga ƙasar.

Wannan kampani, mallakar ƙasar France, shi ne mai tona albarkatun uranium a jihar Agadaz dake arewancin Niger, kazalika, ya na ɗaya daga kampanonin da ke bincike a game da albarkatun ƙarƙashin ƙasa da Allah ya huwacewa Jamhuriya ta Niger.

Gwamnati na zargin Areva da bada tallafi ga yan tawaye da ke ci gaba da tada zaune tsaye a arewacin ƙasar.

A yayin ya ke amsa tambayoyin yan jarida a birnin Libreville, shugaban ƙasar France,Nikolas sarkozy, ya bayyana aniyar shiga tsakanin rikicinAreva da gwamnatin Niger.

A game da haka opishin ministan harakokin wajen France, ya ce ranar litinin mai zuwa, za a shirya taro a birnin Paris, wanda zai haɗa ministar harakokin wajen Niger Aichatu Mindaudu, da takwaran ta na France Bernard Kouchner a game da wannan batu.