Rikici na siyasa a Italiya | Labarai | DW | 23.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici na siyasa a Italiya

Jam´iyyun masu sausauci na Italiya sun amince da marawa, faraminista Romano Prodi baya na yakin da yake na ci gaba da kasancewar sa Faraminista.

Wannan mataki dai ya biyo bayan wani taro ne daya gudana a tsakanin Mr Prodi da yan jamiyyar tasa, a kokarin da ake na ceto shi daga hali na kaka ni kayi daya tsinci kansa a ciki.

Wannan hali dai ya biyo bayan kaye ne daya sha a majalisar dokokin kasar, a game da matakin gwamnatin sa na kasashen ketare.

Wannan dai kuduri daya sha kaye kansa ya kunshi, batu na karin sojin kasar dubu biyu izuwa Afghanistan, a hannu daya kuma da bawa Amurka dama na fadada karfin sojin ta a kasar ta Italiya.

A yanzu haka dai shugaba Giogio Napolitano na gudanar da tattaunawa iri daban daban, don sanin matakin daya kamata ya dauka. Na ko dai ya bukaci Mr Prodi kafa wata sabuwar gwamnatin hadaka ,ko kuma ya kira a gudanar da sabon zabe.