Rataye mutane 6,bisa hukuncin kisa a Iran | Labarai | DW | 06.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rataye mutane 6,bisa hukuncin kisa a Iran

A yau ne aka zatar da hukuncin kisa ta hanyan rataya wa wasu yan kungiyar adawa guda shida a kasar Iran.An zatar da wannan hukunci bisa samunsu da laifuffukan sace sacen baki yan yawon shakatawa,da suka hadar da jamusawa guda biyu a 2003,inji jaridar Etemad ta kasar.Rahotan yayi nuni dacewa wadanda aka ratayen,membobin kungiyar yan tarzoma ne,akarkashin jagorancin Abdolmalek Rigi,na darikar Sunni.An dai samesu ne da laifin kaiwa motar yansanda hari,inda suka kashe mutane 4,cikinsu jamian yansanda uku,kafin su sace Yan yawon shakatawan guda uku,dake kann hanyarsu zuwa Iran.