Rashin ingancin rayuwa a iyakar Najeriya da Kamaru | Zamantakewa | DW | 24.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Rashin ingancin rayuwa a iyakar Najeriya da Kamaru

Mazauna kan iyakar jahar Adamawa a Najeriya da ke makwabtaka da kasar Kamaru na kokawa kan rashin inganci rayuwa duk da irin alfanun huldar kasuwanci da ke a tsakanin yankunan biyu.

 

Hakika makwabatakan Kamaru da Najeriya musamman Jihar Adamawa na daya daga cikin wanda za'a iya cewa na kut da kut ne don baya ga auratayya da huldar kasuwanci dake a tsakaninsu akwai batun addini da al'adu wadanda ke kara hada kan al'umomin biyu  na yin muamala da juna. Malam Aminu Ahmed Yaro, wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, ya ce akwai wasu mastalolin dake tarnaki a daddadiyar danganataka a tsakanin kasashen biyu ta fuskar kasuwanci idan aka yi la'akari da rashin ababen more rayuwa matsalar da ya ce yana faruwa ne don nisan da suka yi da fadar gwamnatoci abinda ya sa ake mantawa da su a wannan bangaren, ya kara da cewa matsalar tana kokarin zama karfen kafa ga mazauna kan iyakar kasashen biyu.

Baya ga batun kasuwanci, jahar Adamawa da Kamaru na alfahari da yadda suke anfani da harshen Fulatanci, wanda kusan shi ne harshen da ya fi rinjaye a dukkan bangarori da ke iyaka da juna yayin da a bangaren sarautar gargajiya kuwa, har a yanzu wasu sarakunan Arewacin Kamaru ke ci gaba da yin mubaya'a ga Lamidon Adamawa. A shekarun baya bayan nan rikicin Boko Haram ya kawo tarin mastaloli a huldar kasuwanci dama zamantakewa ganin yadda ake samun matsalolin zirga-zirga tsakanin Najeriya da Kamaru bisa barazanar tsaro da yankunan biyu suke fuskanta daga ayyukan 'yan ta'addan.