Rasha ta zurawa Saudiyya kwallaye 5 | Labarai | DW | 14.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta zurawa Saudiyya kwallaye 5

A wanna Alhamis din ce aka fara gasar cin kofin duniya na kwallon kafa wadda Rasha ke daukar bakunci. A yi wasan farko ne tsakanin Saudiyya da Rasha inda ake jefawa Saudiyya kwallaye biyar

'Yan kwallon kafar Rasha sun lallasa takwarorinsu na Saudiyya da ci biyar da nema a wasan farko na cin kofin duniya na kwallon kafa da aka fara a yau din nan a kasar ta Rasha. Iury Gazinsky ne ya fara jefawa Rasha kwallonta ta farko a wasa a minti na 12 da fara wasa yayin da Denis Cheryshev ya jefa kwallo na biyu jim kadan kafin tafiya hutun rabin lokaci. Sauran kwallayen kuwa an jefasu ne bayan da aka dawo hutun rabin lokaci.