Rasha ta zargi Amirka kan hari a Siriya | Labarai | DW | 21.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta zargi Amirka kan hari a Siriya

Amirka ta Rasha suna ci gaba da zargin juna kan tashe-tahsen hankula da ke ci gaba da ritsawa da Siriya.

A wanna Laraba Rasha ta yi zargin cewa akwai jirgin mai sarrafa kansa na kawance da Amirka take jagotanta da ya yi shawagi kusa da tawogar kayan agajin jinkai da aka kai hari. Sai dai mai magana da yawun rundunar sojin Rasha bai fito fili ya zargi Amirka da kai harin wanda ya janyo mutuwar ma'aikatan agaji.

Tun farko wani jami'in Amirka ya zargi mahukuntan Moscow da kai harin. Amma Rasha ta zargi Amirka da neman kawar da kan mutane bisa hakikanin abin da ya faru, wanda ya janyo mutuwar kimanin ma'aikatan agaji 20.

A wani labarin Faransa ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta hukunta gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta Siriya wajen saka mata takunkumi saboda amfani da sinadari mai guba.