1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Rasha ta rusa tsarin MDD na saka ido kan Koriya

Abdourahamane Hassane
March 29, 2024

Rasha ta yi amfani da karfin fada a jin da take da shi a MDD wajen rusa tsarin sanya ido kan takunkumin majalisar kan Koriya ta Arewa da shirinta na nukiliya,

https://p.dw.com/p/4eFz6
Hoto: Andrew Kelly/REUTERS

 Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kakaba wa Koriya takunkumin saboda shirinta na nukiliya tun a shekarar ta 2006, wanda aka kara karfafashi a shekara ta  2016 da 2017. Amma tun daga shekarar ta 2019, Rasha da China, musamman ma saboda halin da ake ciki na jin kai na al'ummar Koriya ta Arewa, suka yi kira da a rage wannan takunkumi wadanda ba ya da ranar karewa. Duk da dage kada kuri'ar  da aka yi na ba da damar yin shawarwari, Rasha ta ki amincewa da daftarin kudurin da ya tsawaita wa'adin wannan kwamiti da shekara guda.  Kuri'u 13 ne suka amince da kudurin, yayin da China ta ki kada kuri'a. Amirka da kasashen kungiyar tarrayar Turai sun yi Allah wadai da matakin na   Rasha.